Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Zimbabwe Na So A Cire Sunan Mugabe Daga Filin Jirgi


Filin Jirgin Robert Mugabe
Filin Jirgin Robert Mugabe

Kungiyar tsoffin sojojin kasar Zimbabwe sunyi kira ga gwamnatin kasar da ta chanza sunan filin saukar jirgin saman kasar daga sunan tsohon shugabanta Robert Gabriel Mugabe, inda a cewar su bai chanchanta a sakawa filin sunan shi ba, wanda aka sa a shekarar ta ta gabata kafin aka tilasta mishi sauka daga karagar mulki.


“ Ina ganin chanja sunan filin jirgin sama saboda dalilin da ya sahfi mutane ba dalili ne me kyau ba, wannan ina ganin banbancin siyasa ne wanda ya shafe su, bana ganin hakan abu ne me kyau ga kasar,” a cewar wani jami'i.


Kungiyar tsiffin sojojin tace bai kamata wadanda suka kawo ziyara kasar su fara cin karo da sunan da ke da alaka da mulkin mallaka da tursasawa ba”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG