Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Tsohon Shugaban Yakin Neman Zaben Trump, Paul Manafort da Laifin Zamba


manafort

Kalubalen siyasar shugaban Amurka Donald Trump ya karu yau Talata bayan da tsohon manajan yakin neman zaben sa, Paul Manafort ke fuskantar hukuncin zuwa gidan yari.

Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna bacin ransa yau Talata akan samun tsohon shugaban yakin neman zabensa, Paul Manafort da aikata manyan laifuka, wanda yanzu zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru masu yawa.

“Wannan abin bakin ciki ne,” abinda Trump ya fadawa manema labarai kenan a tashar jiragen saman Charleston, a jihar Virginia ta Yamma, ya kara da cewa yana bakin cikin abinda ya faru ga Manafort, wanda wani gungun masu yanke hukunci suka same shi da laifuffuka har guda 8 na aikata zamba.

Sai dai kuma masu yanke hukuncin a birnin Alexandria dake jihar Virginia, bayan sun kwashe kwanaki 4 suna muhawara, sun kasa iya cimma matsaya akan sauran laifuffuka 10 da ake tuhumar Manafort da su , abinda yassa alkalin kotun zartad da hukuncin cewa ba za’a iya yanke wani hukunci a kansu ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG