Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Zata Gina Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas da Kawar da Talauci-Garba Shehu


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Jihohin Adamawa Borno da Yobe na cikin jihohin arewa maso gabas da ta'adancin kungiyar Boko Haram ya fi daidaitawa cikin shekaru shidan da suka gabata.

Sake gina tattalin arzikin jihohin arewa maso gabas musamman Adamawa, Borno da Yobe abu ne da yake cin ran Shugaba Buhari. Burinsa ne ya sake farfado da tattalin arzikin yankin da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Banda jihohi ukun nan dake arewa maso gabas an hada bukatar sake gina tattalin arzikin jihohin Filato da Kaduna saboda su ma rikicin ya yi masu barna.

A jihohin nan uku na arewa maso gabas da jihohin Filato da Kaduna an kone asibitoci da wuraren ibada kamar coci da masallatai. Haka ma an kone makarantu da tituna da gadoji. Kasuwanni ma basu tsira ba. Yawanci an lalatasu.

Gwamnati na fatan sake ginasu tare da abun da kasar ke dashi da kuma taimakon kasashen waje. Shgaban kasa zai zauna da bankin duniya akan lamarin da kuma asusun bada lamuni na duniya ko IMF a takaice. Zasu nemi hanyoyin da za'a bi a farfado da jihohin da rikici ya daidaita da kuma talauci ya yi masu katutu.

Mugun talauci ne ya baiwa rikicin Boko Haram gindin zama. Ko an yi maganin rikicin Boko Haram idan ba'a kawar da talauci ba to ba'a yi komi ba, tamkar an kashe maciji ne ba'a sare kansa ba. Dole a fuskanci talaucin dake damun talaka da yanayin rayuwa kafin a ce an samu nasara.

Za'a fito da wani shiri da zai inganta rayuwar talaka domin shi ma ya san ana yi dashi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG