Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Chana Ta Saki Tsohon Farfesan Da Ta Kama


Sun Wenguang
Sun Wenguang

A yau litinin ne wadansu na kusa da Wani tsohon Farfesa dan kasar China wanda jami'ai suka yi awon gaba da shi a lokacin da ake tattaunawa da shi kai tsaye a gidan talabijin din sashen Mandarin na Muryar Amurka kusan makonni biyu da suka wuce, suka shaida wa muryar Amurka cewa, ya samu damar komawa gida karkashin matsanancin tsaro.

Sun Wenguang mai shekaru 84 ya shaidawa abokan sa cewa, bayan da aka tsare shi a ranar 1 ga watan Agusta an kai shi wurare da dama, ciki har da wani katanfaren gida dake kan tsaunin Yanzi a yankin sojoji na Jinan, da wani hotel dake garin Jinan a Gabashin China, kasar shi ta haihuwa. An kaishi wurare hudu inda kowanne yake kwana daya zuwa kwanaki biyu karkashin tsaro.

Bayan da aka yi Magana dashi a yau, abokan sun ce ya umarce su da su kira Muryar Amurka su shaida musu cewa, ya koma gida cikin koshijn lafiya. Sun kara da cewa Wenguang ya shaida musu yadda jami’an tsaro suka bincike gidan shi suka kuma dauke duka wayoyin tarho da na tafi da gidanka da na’urar komfutar sa. An kuma toshe shafukan sa na sada zumunci bisa ga cewar abokansa.

Muryar Amurka tayi kokarin Magana da Wenguang a yau din nan, amma abin ya ci tura, jami'an China kuma sun ki su ce komai akan lamarin.
Farfesan ya koma gida bayan da tsofaffin daliban jami’ar Shandong dake China inda ya koyar sheekaru da yawa da suka wuce, suka rubuta budaddiyar wasika ga jami’an, inda sukai kira ga makarantar da ta tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya da kuma ‘yanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG