Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Iran Ta Yi Kiran Da A Yi Gangamin Nuna Kiyayya Ga "yan Adawa

Supporters of ousted President Mohamed Morsi attend Friday prayer at Nasr City, where protesters have installed their camp and hold daily rallies in Cairo, July 26, 2013.
Supporters of ousted President Mohamed Morsi attend Friday prayer at Nasr City, where protesters have installed their camp and hold daily rallies in Cairo, July 26, 2013.

Wata sanarwar wata majalisar Malaman addinin kasar Iran ta yi kiran da a yi gawurtaccen gangami a birnin Tehran a ranar Jumma’a, don bayyana abin da ta kira “kiyayyarta” ga ‘yan gwagwarmayar nemar sauyin da su ka yi zanga-zangar kwana guda ta kin gwamnati a farkon wannan satin.

A wata sanarwarta ta yau Laraba, Majalisar Kula da Aikin Yada Musulunci ta yi kira ga mazauna birnin Tehran da su shiga shiga zanga-zangar bayan Sallar Jumma’a don su bayyana fushinsu kana bin da ta kira laifin jiga-jigan cin amanar kasa da sauran mukarrabansu bijirarru.

‘Yan Majalisar Dokokin Iran masu tsattsauran ra’ayi sun zargin shugabannin masu gwagwarmayar nemar sauyin Mir Hossein Mousavi da Mehdi Karroubi da laifin cin amanar kasa saboda shirya zanga-zangar kin gwamnati da ta tara dubban mutane bisa titunan Tehran da sauran birane ran Litini. Cin amanar kasa laifi ne a kasar Iran wanda hukuncinsa kisa ne.

Babban mai gabatar da kara na Iran Gholam Hossein Ejei ya fadi yau Laraba cewa ya goyi bayan kiraye-kirayen cewa a hukunta ‘yan gwagwarmayar neman sauyin.

Shugabannin ‘yan adawan sun fitar da wasu jawaban nuna turjewa a yau Laraba, a inda Karroubi ke cewa ya na shirye ya sadukar da komi don kasarsa, a inda shi kuma Mousavi ya bayyana zanga-zangar da cewa wata babbar nasara ce. Sun shirya zanga-zangar ce don su bayyana goyon bayansu ga zanga-zangar kwanan nan das u ka yi sanadin hambarar da shugabannin masu kama karya a Misra da Tunisia.

Zanga-zangar ta ranar Litini it ace ta fi girma a Iran tun bayan 2009, lokacin da Mousavi da Karroubi su ka jagoranci wata zanga-zanga mafi girma kan sakamakon zaben da ake takaddama a kai day a sake maido da shugaba Mahmoud Ahmadinejad.

XS
SM
MD
LG