Accessibility links

Gwamnatin Jihar Gombe ta sa Sofofin Ma'aikata Cikin Farin Ciki


Gombe, Najeriya

Ma'aikatan ta suka yi ritaya a Najeriya sukan sha wuya kafin ma a biya su kadan cikin hakinsu. Haka ma ta kaya a lokacin gwamnatocin da suka shude a jihar Gombe. Amma gwamnati mai ci yanzu ta biya duk 'yan fansho kudaden da suke bin gwamnatin lamarin da canza rayuwarsu.

A Najeriya daya daga cikin matsalolin da wadanda suka bar aiki ke fuskanta bayan sun kammala wa'adin aikinsu shi ne na rashin biyansu kudin fansho da kudin barin aiki ko gartuity a takaice.

Yawanci da yawa 'yan fansho kan kwashe shekara da shekaru basu sami kudinsu ba. Amma bincike ya nuna cewa galibin kudin 'yan fansho kan salwanta ne ko kuma a karkata akalan kudaden zuwa wasu ayyuka. Jihar Gombe na daya daga cikin jihohin da ma'aikata musamman na kananan hukumomi suka shiga cikin wani mawuyacin hali. Sabili da haka ya sa gwamnatin jihar ta yanke shawarar biyan ma'aikatan hakinsu sabanin yadda gwamnatocin baya sukai ta kokawa da rashin kudi a matsayin dalilin da ya sa suka kasa biyan ma'aikatan.

Babban sakataren hukumar fansho ta jihar Malam Awal Umar Musa bayan ya kammala biyan duk 'yan fansho ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu cewa "Dama saboda wasu dalilai wannan kudin baya isa a biyasu amma da aka yiwa mai girma gwamna Dr Ibrahim Dankwambo bayani ya sa kwamiti ya tantance basusuka da suke bi ganin haka da tausayi irin nasa da kuma adalci da yake dashi ya sa duk wanda suka yi ritaya daga karamar hukuma a soma biyansu tun daga watan Janairu"

Dangane da kudaden shekarun baya Malam Musa yace suna shirin biyansu. Muhammed Makama tsohon ma'aikaci yace biyan da aka yi hakika sun ji dadinsa kuma sun gamsu da yadda ake biya, yace "domin basu danne mana hakinmu ba. Sun biyamu komi yadda ya kamata"

Shi ma Malam Adamu Mamman yace yayi aiki na shekarau 35 a matsayin malamin makaranta. Yace "a wannan hali da muka samu kanmu na farin ciki alhamdu lilahi an biya wannan abun cikin kwanciyar hankali kowa yana murna...Abun farin ciki ne gaskiya. Muna yiwa gwamna addu'a"

Ita ma Asima'u Dan Bappa tace "Lokacin da muka yi ritaya ba fansho ba gratuity matsaloli suka yi yawa. Muna nan muna ta addu'a dai...Gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya kuma tausaya mana ya samu cikin payroll mu fara karbar fansho domin da can bamu san inda muke ba.

XS
SM
MD
LG