Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janaral Murtala Muhammed ya Yaki Cin hanci da Rashawa a Najeriya


Filin jiragen sama a Lgas da aka sama suna Murtala Muhammed domin tunawa da Janaral Murtala Muhammed
Filin jiragen sama a Lgas da aka sama suna Murtala Muhammed domin tunawa da Janaral Murtala Muhammed

Ranar 13 ga wannan watan aka shirya kasidun tunawa da marigayi Janaral Murtala Muhammed wanda ya rasa ransa a wani kokarin juyin mulki na shekarar 1976

A shekarar 1976 ranar 13 ga watan Fabrairu aka kashe Janaral Murtala Muhammed a Legas bayan ya yi kwana 200 kacal yana mulkin Najeriya.

Ranar 13 ga watan nan aka gudanar da lacca a zauren taro na dakin karatu na gidan Murtala Muhammed dake Kano. Masana kan harkokin siyasa da mulki da dai sauransu suka hallara a wurin taron wadanda suka yi sokaci kan tarihin Janaral Murtala Muhammed da cigaba da ya kawo cikin kwanaki dari biyu kawai na mulkinsa.

Balarabe Yusuf Babale shugaban kungiyar muryar talaka reshen Kano ya bayyana makasudin shirya laccan. Yace "Irin rawar da Janaral Murtala Muhammed ya taka bai kamata a manta da shi ba...Ya yaki cin hanci da rashawa matukar gaske"

Shi ma Dr. Mahmud Lawal na sashin nazarin kimiyar siyasa a Jami'ar Bayero dake Kano wanda ya bada mukala kan tarihin marigayin inda ya ce mutuwar Janaral Murtala Muhammed ta mayarda Najeriya baya da shekara talatin. Yace " A fannin cin hanci da rashawa abun da Murtala ya yi shi ne a maganta abun kuma ayi gyaran da a gaba wasu ba zasu yi ba saboda a tunanensa cin hanci da rashawa zai iya dakile kasa" Ya kara da cewa idan za'a bi gaskiya cin hanci da rashawa ke mayarda mu baya. Yace "Da Murtala ya yi shekaru taran da Gowon ya yi ko takwas din da Babangida ya yi watakila da Najeriya ta zama daban saboda shugabanci ya zo ya nuna na gari kuma shugabanci na misali"

A nashi sokacin Alhaji Abdulkarim Dayabu shugaban rundunar adalci ta Nageriya cewa ya yi halin da Najeriya ta shiga biyo bayan kaucewa hanyar da Murtala ya dorata a kai laifin talaka ne."Tarihi ya nuna talakawa ne a koina suke juyin juya hali basu ake juyawa ba" Yace idan lokacin mulkin mallaka na turawa talakawa sun kori bature suka dawo da sarakuna babu abun da zai hanasu musamman idan aka lura da dimbin jami'o'i da muke dasu yanzu.

Alhaji Hudu Bello Denga shugaban kungiyar rundunar adalci reshen Taraba yace manufarsu da ta kungiyar talaka daya ce. Yayi fatan duk wadanda suka halarci taron zasu san wanene Murtala Muhammed da kuma irin ayyukan da ya yi wa Najeriya kuma su yi koyi da shi.

A karshe an bukaci yan Najeriya sun dinga tunawa da Janaral Muhammed da aikin da ya yi da halayansa musamman yadda ya mayarwa kasar dukiyoyin da ya mallaka.
XS
SM
MD
LG