Accessibility links

Malaman Kwalajin Kimiya da Fasaha Mallakar Jihar Neja Sun Koka da Gwamnati


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Cikin 'yan kwanakin nan kwalajin kimiya da fasaha mallakar jihar Neja dake Minna sai fadawa wasu matsaloli yake yi kama daga kashe wani malami zuwa ga dukan ma'aikaci

Malaman kwalajin kimiya da fasaha ta jihar Neja sun kirawo taron manema labarai inda suka ce gwamnatin jihar tamkar ta yi watsi da su tare da makarantar.

Shugaban malaman kwalajin Ibrahim Muhammed ya yi karin haske kan halin da kwalajin ke ciki da kuma dalilin da ya sa suka kira manema labarai. Yace 'Kamar yadda na fada a jawabina gwamnatin jihar tana yi kamar makarantar ba tata ba ce. Ta kafa makaranta.Muna nan muna aiki amma ta yi kaman ba ita ta kafa makarantar ba. In za'a duba kaman welfare na malamai ba ruwansu. Dakunan bincike da ake anfani da su babu wani gyara ko sayen kayan aiki...Ba'a turawa makarantar kudi shi ne muka ce bari mu zo mu sanarda duniya inda makarantarmu take. Idan da ba' fadawa wanda ya kamata ya ji to idan mun fadawa duniya shi ma zai ji"

Kawo yanzu dai akwai yajin aikin gama gari na kungiyar malaman kwalajin kimiy da fasaha to sai dai koda kungiyar ta kasa ta janye yajin aikin su na Neja ba zasu janye ba sai an biya bukatunsu wadanda suka shafi makarantarsu.

A nata gefen gwamnatin jihar Neja tayi watsi da kalamun malaman. Dr Bashar Abdullahi kwamishanan ilimi mai zurfi yace "A kowane lokaci mu kan zanta da su kuma mun gama duba irin wanda zamu iya biya kuma mun gaya masu. Abun da ya rage shi ne mu ga lokacin da zamu yi kari, kari kuma kaman gine-gine"

Kwamishanan ya kara cewa ba gaskiya ba ne a ce gwamnatin jiha bata kula da su ba. Yace sun ma ba kwalajin izinin yin anfani da duk kudin da suka tara maimakon su baiwa gwamnati kamar yadda doka ta tanada.

XS
SM
MD
LG