Accessibility links

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta Karbo Bashin Naira Milyan Dubu Biyar Domin Ayyukan Raya Kasa

  • Aliyu Imam

Kasuwar saye da sayar da hannayen jari ta Najeriya.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta karbi Bashin Naira Milyan Dubu Biyar Domin Ayyukan Raya kasa.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta karbi Bashin Naira Milyan Dubu Biyar Domin Ayyukan Raya kasa. Gwamnan jihar Alhaji Umaru Tanko Almakura ne ya bayyana haka a bikin sanya hanu kan yarjejeniyar karbar bashin daga hanun bankunan Fidelity, da IBT Stanbic Bank da kuma Mainstreet a Abuja.

Gwamna Almakura yace gwamnatins a zata yi amfani da kudaden ne wajen gyara gine ginen makarantu da suka lalace da kuma ayyukan kasuwanni da ba'a kammala ayyukansu ba cikin jihar.

Gwamna Tanko yace jihar ta gaji basussuka na Naira Milyan dbu 37 daga gwamnaotic da suka shude, kuma duk ta biya su. kuma tana fatan zata mikawa gwamnati mai zuwa tsari da zai bata ikon walwala.

XS
SM
MD
LG