Accessibility links

Gwamnoni 7 Daga Cikin 19 Na Bangaren Amaechi Su Na Halartar Taro Da Kansu a Sokoto


Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi.

Shugaban kungiyar gwamnonin ta Najeriya yace taron nasu ba ya da nasaba da rade-radin cewa su dake yin takaddama da PDP-Tsohuwa su na neman mafita ne

Gwamnonin jihohi 7, da mataimakan gwamnonin wasu jihohin 5 su na halartar taron kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Rivers a Sokoto.

A lokacin da yake bude taron, shugaban kungiyar ta gwamnonin Najeriya, gwamna Amaechi, ya musanta hasashen da wasu keyi cewa gwamnonin PDP guda 7 dake takaddama da PDP-Tsohuwa mai samun goyon bayan shugaba Goodluck Jonathan, su na son yin amfani da wannan taron ne domin tsara alkiblar da zasu dosa.

Mr. Amaechi yace wannan taron ba wai kawai na nazarin halin da kasa take ciki ba ne, wata dama ce ta nazarin irin kalubalen dake fuskantar jihohin kasar a wannan lokaci. yace wannan gafaka ta gwamnoni zata kuma nazarci yadda za a iya kyautata rayuwar talakan Najeriya.

Mai masaukin baki, gwamna Aliyu Magatakarda Wammako na jihar Sokoto, yace Najeriya tana wani matsayi na gaba kura baya siyaki, don haka wajibi ne kan kowane dan kasa ya taka rawa wajen ceto ta daga fadawa ramin da ba zata iya fitowa daga ciki ba.

Shugaban babban Bankin najeriya, Sanusi Lamido Sanusi, da mai ba shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaron kasa, Sambo Dasuki, ba su bayyana a wurin tyaron ba har zuwa lokacin da wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna ya aiko mana da rahoto, duk da cewar an shirya zasu gabatarwa da taron kasidu.
XS
SM
MD
LG