Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Saki Mutum 27 da Suka Kama a Kamaru


Shugaban kasar Kamaru Paul Biya.
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya.

A cikin su har da matar mataimakin firai ministan kasar da kuma 'yan kasar Sin 10.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya ce an saki wasu mutane ishirin da bakwai da wasu mayakan da ake zargi 'yan Boko Haram ne su ka kama a farkon shekarar nan su na yin garkuwa da su, a cikin mutanen har da 'yan kasar China goma masu aiki a kasar ta Kamaru.

Shugaba Paul Biya ya fada Asabar din nan cikin wata sanarwa cewa mutanen sabbin kubutarwa wadanda suka hada har da matar mataimakin firai ministan kasar Kamaru, su na nan lafiya.

Mr.Biya ya ce an mika mutanen ne ga hukumomin kasar Kamaru, kuma ya ce a cikin watannin Mayu da Yuni aka kama su a garuruwan Waza da kuma Kilofata.

Kasar Kamaru ta hada kan iyaka mai tsawo da kasar Najeriya inda 'yan Boko Haram ke mummunan boren zubar da jini tun shekarar dubu biyu da tara.

Kungiyar Boko Haram aka dorawa laifin kisan dubban mutane a fadin yankin arewacin Najeriya, kuma ita ce ta dauki alhakin sace 'yan mata fiye da maitan daga garin Chibok a cikin watan Afrilu, al'amarin da ya hasala kasashen duniya.

Har yanzu dai gwamnatin kasar Najeriya na faman neman kawo karshen hare-haren, duk kuwa da dubban sojojin da ta zuba a arewa maso gabashin kasar tare da kafa dokar ta baci a jahohi uku da suka hada da Borno, da Yobe da Adamawa.

Sojojin Najeriya (File Photo)
Sojojin Najeriya (File Photo)

XS
SM
MD
LG