Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Bada Umarnin A Bindige Duk Wanda Ya Yi Yunkurin Fasa Gidan Yari


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

Gwamnatin Najeriya ta umarci jami'an kula da gidajen gyaran hali a kasar su bindige duk wani mutumin da ya yi yunkurin fasa gidajen yari a ko ina cikin kasar.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Ogbeni Abdulra'uf Arebesola ya bada umarnin ne yayin da yake jawabi ga jami'an hukumar kula da gidajen gyaran halin yana jaddada cewa dolene a hana duk wani ko wasu tsageru dake neman balle gidan gyaran hali.

Mninstan yace ba za a taba amincewa da farmaki akan ire-iren wadannan gidaje ba, yana mai bada umarnin lalle a harbe har lahira duk wanda ya yi gangancin fasa gidajen yari, ta yadda ba zai rayu ba balle ya bada labari sai dai abada labarinsa.

Arebesola ya kara da cewa gidajen gyaran hali wasu cibiyoyi ne da ke a matsayin ginshikan kyautata tsaron al'ummah don haka dolene a yi duk wani abu mai yiwuwa wajen samar da ingataccen tsaro a cibiyoyin

A Najeriya dai yan ta'adda na ta kai farmaki a gidajen yari a sassa daban-daban na kasar don kubutar da abokan tafka ta'asarsu dake tsare a gidajen, al'amarin kuma dake tayar da hankalin gwamnati da al'ummar kasar.

A dai galibin irin wannan yanayi manyan masu tafka laifuka ne ke tserewa sannan su koma su ci gaba da uzurawa mutane ta hanyar sake shiga wani sabon zagaye na aikata manya kuma miyagun laifuka.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko wannan umarni na ministan zai taimaka wajen shawo kan matsalar yawan kai hari da fasa gidajen yarin.

XS
SM
MD
LG