Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Kaddamar Da Wani Sabon Tsari Kan Ruwa A Kasar


Madatsar ruwa
Madatsar ruwa

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da shirin manufar kasa kan ruwa a wani taro da ya hada da gwamnoni da Kwamishinonin ruwa na kasar.

An gudanar da taron ne a birnin tarayya Abuja, da yake jawabi mataimakain shugaban Najeriya yace an tsara wasu matakai a wani habbasan tunkarar kalubalen da ake fuskanta fannin ruwa, ya kuma ce duk da amfanin da ruwa ke da shi a ga rayuwar bil Adama abin mamaki ne yadda ake daukar batun ruwa da sakaci. Idan ruwa yayi yawa ko yayi karanci matukar ba a dauki wani mataki akai ba ka iya saka rayuwar dan Adam da muhalli cikin wani hali.

Shima a jawabinsa ministan albarkatun ruwan Najeriya, Injiniya Sulaiman Husaini Adamu, yace tuni Majalisar Zartarwa ta amince da wani kundin daftari da za a mikawa Majalisar Tarayya.

Masu samar da wutar lantarki daga albarkatun ruwa musamman Madatsu na matukar bukatar ruwa sosai, yayin da su kuma Manoma ke kokawa kan cewa duk lokacin da aka sako ruwan yana yin yawa. A cewar gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Madatsun ruwa suna da amfani ga Manoma da kuma masu aikin samar da wutar lantarki, yayin da masu samar da wuta ke son Dam ya cika, su kuma Manoma idan ruwan ya cika yana zuba ya bata musu amfani gona, kaddamar da wannan kuduri zai taimaka wajen samar da wuta da kuma amfanin gona.

Farfesa Yemi Osinbajo, yace kididdiga ta nuna kimanin sama da ‘yan Najeriya Miliyan 66 ne ke basa samun ingantaccen ruwan sha mai tsafta, kuma al’amarin yafi tsananta a yankunan karkara inda gurbatattun makwantan ruwa da kuma rafi kan zama hanyar da ake samun ruwa domin sha da sauran amfanin yau da kullum na gida.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00

XS
SM
MD
LG