Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Zaben Amurka Ke Gudana A Jihar Pennsylvania


Wata ma'aikaciyar zabe a jihar Pennsylvania

A yayin da Amurkawa ke fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’un zaben sabo ko sabuwar shugaban kasa, mai cike da dinbin tarihi.

Wannan dai shine karon farko da aka taba samun mace ta zama ‘yar takarar babbar jami’iyar daya daga cikin jam’iyyun Amurka. Haka kuma an sami hamshakin mai kudi da bai taba rike kowanne irin mukamin siyasa ba, ya tsaya a matsayin dan takarar babbar jam’iyya.

Wakilin shashen Hausa na Muryar Amurka a jihar Pennsylvania, Yusuf Aliyu Harande, ya ya zagaya runfunan zabe a karamar hukumar Indiana, domin ganin abubuwan da ke faruwa, kasancewar jihar Pennslvania na daya daga cikin jahohin da suke da matukar muhimanci a zaben kasar Amurka.

Hasashe dai ya nuna babu wani dan takara da zai iya lashe zaben kasar ba tare da ya samu nasara a jihar Pennsylvania. Tun daga karfe 8 na safiyar yau Talata mutane ke ta fitowa maza da mata yara da manya don kada kuri’un su. Yawancin mutanen da Yusuf ya zanta da su sun bayyana cewa wannan zabe ne mai cike da dinbin tarihi. Ana sa ran ka kimanin karfe Goma na dare za a fara samun sakamakon zabe.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG