Accessibility links

Gwamnati Ta Kasa Samar Da Ingantaccen Tsaro - inji APC


Taron shugabannin APC na kasa

A wani taro manema labarai da ta yi a Legas jam'iyyar APC ta bakin shugaban riko na kasa Chief Bisi Akande tace Najeriya ta gaza wurin smarda da ingantacen tsaro a kasar.

Jam'iyyar APC tace 'yan Najeriya da ma kasar gaba daya sun shiga wani halin "wayyo ni Allah" sabili da gazawar da gwamnatin kasar tayi wurin samarda ingantacen tsaro.

A taron manema labarai da jam'iyyar tayi a Legas shugaban jam'iyyar na kasa na rikon kwarya yace gwamnatin Najeriya ta buge da ganin laifukan mutane kawai. Yace yayin da ake kashe 'yan kasar kullum ita kuwa gwamnati sai cewa ta keyi tana nan tana kokarin shawo kan lamarin amma har yanzu 'yan kasar basu gani a kasa ba.

Shugaban APC yace dalili ke nan da suke baiwa gwamnatin shawarar yadda zata shawo kan lamarin. Wasu daga cikin shawarwarin sun hada da tattaunawa da 'yan kungiyar Boko Haram kana akwai bukatar rundunonin tsaro suna da hanyoyi sahihai kuma suna mu'amala da juna wurin tattara bayyanai da musanya rahotannin asiri tsakaninsu. Haka kuma jam'iyyar tace akwai bukatar a takaitawa masu kai hare-hare basu ci nasara ba. Duk inda suka kai hari a magance sake aukuwar hakan. Akwai kuma bukatar cigaba da horas da jami'an tsaro domin fuskantar irin kalubale na yanzu.

Da wakilin Muryar Amurka ya cewa sakataren jam'iyyar na kasa Jari Musa Tursa cewa suna furucinsu ne yanzu domin lokacin zabe na karatowa. An tambayeshi shin me yasa sai yanzu suke magana bayan sun yi shiru da can. Kila suna magana ne yanzu domin su burge 'yan Najeriya cewa zasu fi PDP iya mulki. Sai yace abun da suke magana akai ba abu ne na siyasa ba. Abu ne na zaman kasar cikin lafiya. Yace su a APC suna ganin hakkin gwamnati ne da jami'an tsaro su tabbatar sun kare rayuka da dukiyoyin mutane. Idan babu tsaron ko siyarsar ma ba za'a iya yinta ba.

Mai rike da mukamin ma'ajin jam'iyyar Hajiya Umar Faruk tace abun da uwargidan shugaba ta yiwa wasu jam'an jihar Borno bai dace ba. Tace ita ta dauka lokacin da abun ya faru kafin a ce kwabo an tsinci uwargidan shugaban kasa a Maiduguri akan hanyarta ta zuwa Chibok. Kamata yayi ta je ta zauna da iyayen yaran da aka sace, ta tausaya masu, ta karfasu ta kuma basu tabbacin cewa gwamnatin mijinta zata yi iyakacin kokarinta ta kubuto da yaran.

Amma mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na kasa Ibrahim Jalo yace babu abun da gwamnati zata yi 'yan adawa sai sun yi zargi su kushe. Yace al'ada ce da PDP ta yi kokarin canzata. Misali idan wani gwamna ya tafi kana aka yi sabo to sabon zai yi watsi da duk ayyukan da tsohon yayi bai gama ba. Yace PDP ta kawar da irin wannan halin. Yace to wannan ya gagara samuwa a jam'iyyar APC. Ba zata taba ganin wani abun alheri da jam'iyyar PDP ke yi ba ta kuma yaba.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.
XS
SM
MD
LG