Accessibility links

Daga cikin matakan da shuwagabanni suke dauka a lokutan tashin hankali da rigingimu, akwai ziyarar gani da ido, domin jajantawa da nuna alhini. Tambayar anan itace yaushe Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya zai je Cibok?

Misalin kwanaki 26 da sace daliban Cibok su kusan 300 ran 14 ga watan Afrilu, inda har yanzu ba'a da tabbacin inda mafi yawancin daliban suke. Yanzu dai gwamnatin Najeriya ta bayyana gazawarta wajen nemo daliban, kuma tayi maraba da taimakon kasashen ketare domin tayata aikin neman daliban.

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya ziyarci garin na Cibok bayan faruwar lamarin, inda ya gayawa iyaye da 'yan uwan wasu daga cikin daliban, da mazauna garin cewa shime yana tare dasu a jimami, da bakin cikin lamarin.

Masu kula da al-amuran yau da kullum, sun fara yin tambayoyi akan ko yaushe Shugaba Goodluck Jonathan zai ziyarci wannan gari domin haduwa da iyaye da 'yan uwan wadannan dalibai domin jajanta musu, da kuma ganin irin barnar da 'yan bindigan suka yi wa garin da makarantar Sakandare ta mata.

"Ai Jonathan bai dauki matsalolin mutanen arewa maso gabashin Najeriya a matsayin matsalarshi ba, ko ta gwamnatinshi. Kallon wannan lamari yake a matsayin matsalar arewa kawai. Bai je Yobe ba, bai je Cibok ba. Ba kamar Obasanjo be, shi yana ziyartar inda aka samu matsala," a cewar Awwal Musa Repsanjani, dan rajin kare hakkin bil adama.

"Ai akwai rashin tausayi a lamarin, kuma ya kamata jama'a su dauki matakan kare kansu idan ba'a samu masalahar wannan abun ba, saboda gwamnati ta nuna wa duniya cewa bata damu da arewacin Najeriya ba. Kasuwanci ya tsaya, ilimi ya tsaya, masana'antu sun mutu," a cewar Mr. Repsanjani."Kundun tsarin mulkin Najeriya ya dora tsaron kasa a karkashin shugaban kasa, dole ne sai shine zaiyi wani abu."

Dan rajin kare hakkin bil adama din bai tsaya anan kawai ba, saboda ya tabo batun zargin da akawa gwamnati a cikin wannan rigima.

"Dama ana zargin da hannun gwamnati a abubuwan dake faruwa. Saboda, babu yadda zaka shigar da kayan ta'addanci kamar yadda ake yi, a ce wai ba'a gani ba."

Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin Ministan Yada Labaran Najeriya, Labaran Maku domin ya mayar da martani akan wadannan batutuwan, amma bai dauki wayoyi masu yawa da aka buga mishi ba.
XS
SM
MD
LG