Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Soma Bitar Ayyukan Ministoci Na Tsakiyar Wa’adin Mulkinta Na Biyu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)

Gwamnatin tarayyar Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta soma gudanar da taron bitar ayyukan ministocinta na tsakiyar wa’adin mulki na biyu a birnin taraya Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari a yayin jawabin bude taron bitar, ya sake jadada cewa ya na kan bakarsa na tabbatar da cika alkawuran da ya dauka a yayin gangamin yakin neman zabensa na wa’adin mulki na biyu.

A cikin alkawuran da shugaban ya dauka, akwai samar da kafaffen bunkasa tattalin arzikin kasar, yaki da ayyukan ta’adanci da samar da tsaro, sai yaki da cin hanci da rashawa da dai suransu.

A cikin jiga-jigai daga bangarorin gwamnatin kasar daban-daban da ke halartar taron ban da shugaba Buhari, akwai mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugabannin majalisun tarayyar kasar, sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila da dai sauransu.

A yayin jawabinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce tattalin arzikin Najeriya na kan hanyar kara bunkasa sossai daga zangón farkon shekarar 2019, a yayin da bullar annobar koronabirus a zango na biyu na shekarar 2021 ya yiwa tattling arzikin kasar zagon kasa inda aka sami durkushewar kaso 1.0 cikin 100.

Osinbajo ya kara da cewa bangarorin tattalin arzikin Najeriya da suka sami koma baya matuka sun hada da bangaren sufuri da kaso 49 cikin 100, bangaren kudin shiga na hospitality da kashi 40 cikin 100, bangaren ilimi da kashi 24 cikin 100 a cikin zango na biyu na shekarar 2020.

Taron bitan ministoci a kan ci gaba da ake sami a Najeriya a yanzu
Taron bitan ministoci a kan ci gaba da ake sami a Najeriya a yanzu

Bangarorin gine-gine, shimfita hanyoyi, kasuwanci da cinikayya da dai sauransu duk sun fuskanci koma baya matuka in ji shi.

Takardun kudin kasar ma wato naira, na kan 380 kan kowacce dala a zango na 3 na shekarar 2020 in ji Osinbajo, baya ga matsalar rashin aikin yi da ta kai kashi 33 cikin 100.

Taron bitan ministoci a kan ci gaba da ake sami a Najeriya a yanzu
Taron bitan ministoci a kan ci gaba da ake sami a Najeriya a yanzu

A matakin samo mafita ga matsalolin da suka addabi kasar sakamakon tasirin annobar koronabirus, shugaba Buhari ya kafa kwamitin da zai rika nazari kan ayyukan ma’aikatu da ministoci da kuma shirin tabbatar da bunkasa dorewar tattalin arziki.

Sauran jiga-jigan gwamnati da ke halartar taron da ake yadawa kai tsaye a gidan talabijan na kasa wato NTA da gidan talabijan na Channels, na jiran lokaci ya kawo kan su don gabatar da jawabi kan nasarori da akasi da ake samu a ma’aikatunsu a halin yanzu.

Karin bayani kan taron bitan zai biyo baya….

XS
SM
MD
LG