Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari A Jihar Imo: Kwaikwayon Al'adar Yankunan Da Shugabanni Suka Ziyarta


Buhari 5

“Da alama kuma shugaba Muhammadu Buhari yana ji da kahon da aka ba shi a jihar Imo, domin idan ka duba duk hotunan ziyararsa a jihar, za ka ga a ko ina yana daga kahon sama, in ma kowa bai daga na shi ba."

An dade da shugabanni a kasashe da dama na duniya, suke dabi’ar kwaikwayon al’adun al’ummomin da suka ziyarta, ko da kuwa sun bambanta da na shugabannin.

Wannan al’ada dai tana da dogon tarihi a Najeriya ga kusan dukkan shugabanni musamman na mulkin farar hula, inda suke yin shiga irin ta kabilun da suka kai wa ziyara, kamar yadda lamarin ya kasance a ziyarar baya-bayan nan da shugaba Muhammadu Buhari ya kai a jihar Imo, wadda akasari jama’arta ‘yan kabilar Igbo ne.

Buhari 3
Buhari 3

‘Yan Najeriya da dama sun ga irin yadda Buhari, tun daga saukarsa a filin jirgin sama, yake sanye da tufafi irin na ‘yan kabilar Igbo, da jar hula (dara) da kuma musamman kaho na nuna girma da alamar shugabanci.

Mai sharhi kan lamurran siyasa a Najeriya, kuma malami a jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, Dr. Mansur Isah Buhari, ya bayyana cewa wannan al’ada ta samo asali ne tun sa’adda aka soma fafutukar samun zaman lafiya da hadin kai a tsakanin kabilu a cikin Najeriya.

“A Najeriya shugabanni sun rungumi wannan al’ada ne domin nunawa jama’ar su cewa Najeriya kasa daya ce, al’umma daya” in ji Dr. Mansur Buhari.

Buhari 2
Buhari 2

Ya ci gaba da cewa “idan ka lura, ‘yan kabilar Igbo na cikin yankunan da ake samun turjiya da fafutukar neman ballewa daga Najeriya. To shiga irin ta al’adar su da Buhari, wanda shi ne shugaban Najeriya yayi, yana nuna musu cewa shi shugaba ne na dukkan ‘yan Najeriya, na dukkan kabilun Najeriya, kuma na dukkan mabiya addinai a Najeriya, haka kuma kowa na shi ne.”

“Da alama kuma shugaba Muhammadu Buhari yana ji da kahon da aka ba shi a jihar Imo, domin idan ka duba duk hotunan ziyararsa a jihar, za ka ga a ko ina yana daga kahon sama, in ma kowa bai daga na shi ba. To ko da domin siyasa ne, wannan na nunawa ‘yan kabilar cewa su sashe ne na Najeriya, suna karkashin ikon Najeriya ne, haka kuma Najeriya ta damu da su kamar yadda ta damu da kowane dan kasa,” in ji shi.

Buhari 1
Buhari 1

Dr. Mansur Buhari ya ce duk da yake dai akwai siyasa a cikin irin wannan dabi’ar, to amma tana da kyau, kuma tana da amfani wajen hada kan kasa da ‘yan kasa.

“Bari in ba ka misali. Lokacin mulkin Goodluck Jonathan, ya taba kai ziyara a jihar Sokoto, inda tun a filin jirgi, dimbin jama’ar da suka je tarbonsa kawai suka ga ya fito a cikin riga da jamfa da wando, da kuma hula kube, shiga irin ta cikakken Bahaushe, sabanin irin yadda aka san shi da kananan tufafinsa da malfa.”

“Wannan ya sa tun a nan jama’ar jihar suka dauka cewa lalle nasu ne, suka kuma manta da duk wani bambanci da ke tsakaninsu na addini ko al’ada. Hasali ma, har sunan sa suka yi wa kwaskwarima don ya daidaice da sunan Hausawa.”

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A lokacin ziyarar ta wuni daya dai, shugaba Buhari ya yi wani zaman tattaunawa da shugabannin kabilar ta Igbo da na sauran al’ummar yankin na kudu maso gabashin Najeriya, inda ya jaddada musu cewa babban burinsa shi ne daidaita al’amura a Najeriya ta fuskar tsaro da tattalin arziki.

“Tsaro shi ne abu na farko da za’a fi baiwa muhimmanci, sa’annan kuma sai tattalin arziki. Sai idan jama’a na cikin kwanciyar hankali ne sannan za su iya mai da hankali kan sana’o’insu,” Buhari ya fadawa taron shugabannin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG