Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka Za Su Yi Muhawarar Karshe Kafin Zabe


'Yan Takatarar Shugaban Kasar Amurka Donald Trump da Joe Biden.
'Yan Takatarar Shugaban Kasar Amurka Donald Trump da Joe Biden.

Yau alhamis za a gudanar da muhawara ta biyu kuma a karshe tsakanin 'yan takarar shugaban kasar Amurka kafin zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar uku ga watan Muwamba.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Republican Donald Trump, da abokin karawarsa na Democrat tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, zasu fafata a wata mahawara da yammacin yau Alhamis, kwanaki 12 kafin zaben kasar a ranar uku ga watan Disamba na wani wa’adin shekaru hudu a fadar White House.

‘Yan takarar biyu da dukkanin su suka haura shekaru 70 sun yi ta yiwa juna katsalandan a mahawarar sa’o’i 90 da aka gudanar a karshen watan Satumba da kwararru a harkokin siyasar Amurka suka kwatanta da mafi muni a muhawarar da Trump yafi Biden yin katsalandan.

Muhawarar 'Yan takatar Shugaban kasar Amurka Donald Trump da Joe Biden
Muhawarar 'Yan takatar Shugaban kasar Amurka Donald Trump da Joe Biden

yan-takarar-shugaban-kasar-amurka-sun-tafka-muhawara

trump-da-biden-sun-yi-musayar-zafafan-kalamai-a-muhawararsu

zaben-amurka-na-2020-muhawarar-mataimakan-yan-takara

Amma a wannan karo, hukumar shirya mahawarar shugaban kasa zata rufe abin maganar dan takarar yayin da daya ke maganar mintu biyu na amsa tambayoyi a kan muhimman batutuwa shida da mai jagorantar mahawarar Kristen Walker ta labaran NBC zata rika gatarwa.

shirye shiryen da aka yi da kuma yadda za a gudanar da muhawarar wadda za a yi a wata jami’a a Nashville dake jihar Tannessee sun sauya a kan abin da ya faru a mahawarar farkon. An soke mahawara ta biyu da aka shirya yi a makon da ya gabata bayan da Trump ya kamu da coronavirus aka kuma kwantar dashi a asibiti kwanaki uku.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG