Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Soma Cafke Wadanda Suka Lakume Kudin Hatsi


 Firayim Ministan Nijar Birji Rafini
Firayim Ministan Nijar Birji Rafini

Gwamnatin Nijar ta kan tanadi hatsi lokacin da ya wadata kana idan yayi tsada ta fitar dashi ta rabawa shugabannin garuruwa su sayar da rahusa su mayar wa gwamnati kudin amma a jihar Damagaran wasu shugabannin sun ci amana , amanar kuma ta cisu domin sun shiga hannu hukumomi.

Matakin ba sani ba sabo na yaki da cin hanci da rashawa da almundahana a kasar Nijar ya fara aiki a jihar Damagaran inda aka cafke wasu da suka yi rub da ciki da kudin rumbun tsimi da aka sayarwa jama'a a farashi mai rahusa.

Shugaban gundumar Magarya inda lamarin ya fi kamari saboda yawan wadanda suka yi sama da fadi da kudaden ya bayyana sunayen wadanda suka yi munamunar. Wani cikinsu yana da kudi miliyan sittin da tara na kudin sefa da ya kamata tuni ya mikawa gwamnati amma bai yi ba.

Akwai kuma wanda aka rikeshi akan kudi miliyan goma sha ukku . Duk irin wadannan suna kaso sai sun mayar da abun da suka ci.

Wasu sun biya bayan an turasu gidan kaso. Akwai kuma wanda ya nemi a bashi wa'adi domin ya hada kudin amma kuma yayi ta kare.

Shi magajin garin Tsatsinbari an bashi hatsi na miliyan talatin da takwas amma ko kwandala bai biya ba. Da aka bukaci ya biya kudin sai yace tsohuwarsa bata da lafiya zai kaita Maradi ya dawo. Maimakon hakan sai ya je wani wurin ya dauki kayan da za'a sayarwa talakawa ya sayar ya bace.

Kungiyoyin farar hula da suka ta yin fafutikar ganin an yi binciken kwakwaf akan lamarin sun furta. Ta bakin Sa'adatu Yarmalam ta kungiyar farar hula a jihar Damagaran tace tunda suka dago maganar da duk wanda aka kama ba kudin kawai zai biya ba, a'a, sai ya hada da zama gidan kaso domin zuwa gidan kaso horo ne, ya kuma zama daratsi ga kowa don gobe.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG