Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Pakistan Ta Sasanta Da Kungiyoyin Islama Masu Zanga Zanga.


Masu Zanga znaga a Pakistan
Masu Zanga znaga a Pakistan

Wata tawagar gwamnatin Pakistan ta cimma matsaya da wasu kungiyoyin Musulmi a kan dakatar da wata gagarumar zanga zangar kwanki uku na nuna kalubalantar hukuncin kotun koli da ta saki wata ‘yar Krista da tayi kalaman sabo ga Manzon Allah.

A karkashin wannan yarjejeniyar gwamnati ta amince da daukar matakan doka ta hana wannan mata ficewa daga kasar, yayin da kotu zata saurari karar da aka gabatar mata a kan hukuncin.

Mambobin wata kungiya ta Tehreek e-Labbaik ya Raool Allah ko TLYR a takaice sun rufe hanyoyi a biranen kasar kuma sun yi arangama da ‘yan sanda a cikin dare. A cikin wani hoton bidiyo na wayar salula, an ga wani a cikin masu zanga zangar yana harbi da karamar bindiga.

An fara wannan zanga zangar ne da safiyar Laraba bayan kotun kolin kasar ta amince da rokon Asia Bibi a kan hukuncin aikata laifi da aka yake mata. Bibi dai tana huskantar hukuncin kisa tun cikin shekarar 2010 karkashin dokar kalaman sabo a Pakistan mai tsarkakkiya.

Bibi dai tace an yi mata kage ne biyo bayan wata zazzafar musu da suka yi da wasu mata da suka ki shan ruwa da ta basu saboda ita ‘yar Krista ce.

Akwai wasu kungiyoyin addinai da su ma suka yi zanga zangar lumana a jiya Juma’a

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG