Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Ta Musunta Maganar Baiwa Rasha Bayanan Sirri


Babban mashawarcin Amurka kan harkokin tsaron kasa, H.R. McMaster da wadansu jami’an gwamnati shugaba Donald Trump sun musanta sahihancin rahotannin da ke nuni da cewa, shugaban kasar ya gayawa jami’an kasar Rasha wadansu bayanan sirri a ofishinsa dake fadar shugaban kasa.

McMaster ya shaidawa manema labarai a harabar fadar White House jiya litinin cewa, rahoton da aka fara bugawa a jaridar Washington Post, bashi da tushe. Ya kara da cewa “babu wani lokacin da aka tattauna a kan hanyoyin tara bayannan leken asiri kuma shugaban kasar bai fallasa wani tsarin aikin soji da ba a riga aka sani ba”.

Kafofin watsa labarai da dama sun bada rahoto cewa, shugaba Trump yayi wani bayani da ake dauka a matsayin na matukar sirri yayin ganawarsu a ofishisa.

Shugaban Amurka yana da ikon bayyana kowanne irin rahoton sirri, saboda haka abinda Tump ya yi bai keta doka ba. Sai dai jami’an leken asiri da jaridun suka ambata sun bayyana damuwa cewa, bayanin zai iya kawo cikas a dangankatar dake da matukar mahimmanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG