Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Arewa Tayi Gwajin Makami Mai Nisan Zango


Kasar China ta bukaci da a kai zuciya nesa domin hana karin aukuwar zaman tankiya a yankin

Yau Lahadi kasar Korea ta arewa tayi gwajin harba wani makami mai linzami a nisan ba saban ba dake nuni da kila wani sabon tsari mai matakai biyu da zai yi zuwa nisa kilomita dubu hudu da dari biyar, kasar ta kaddamar.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta fada a wata sanarwar data gabatar, cewa wannan gwaji ya zama tamkar kira ne ga kasashen duniya da su kaddamar da takunkumi mai tsanani akan Korea ta arewa.

Tunda farko kasashen Japan da Korea ta kudu sunyi Allah wadai da matakin na Korea ta arewa a zaman baban barazana ga yankin kuma keta ka’idar kudurorin Majalisar Dinkin Duniya akan shirin makamai na kasar.

Kasar China ta bukaci a kai zuciya nesa domin hana karin aukuwar zaman tankiya a yankin, a yayinda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta baiyana rashin goyon bayan ta ga keta ka’idodin kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da Korea ta arewa ta yi.

Kasar China ce kawai babar kawar Korea ta arewa kuma abokiyar huldar kasuwancinta a yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG