Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Cece Kuce Kan Zargin Sayo Makamai da Jirgin Shugaban CAN


Shugaban kungiyar Izala Sheihk Abdullahi Bala Lau.

Har yanzu ana samun cece kuce kan zargin yinkurin sayo makamai da jirgin Shugaban kungiyar Kiristan Nijeriya Ayo Oritsejafo.

Shugaban Kungiyar Izalatul Bid’a Wa’iqamatus Sunna Sheihk Abdullahi Bala Lau ya ce binciken batun jirgin saman Shugaban Kungiyar Kiristan Nijeriya (CAN), Rev. Ayo Oritsejafor da aka samu dauke da kudi mai yawa na sayo makamai, na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmi.

Wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhikaya ya ruwaito Sheikh Lau na cewa ya kamata Shugaban kasa da jami’an tsaro da Majalisar Tarayya su binciko matsayin jirgin da matsayin kudin da kuma matsayin makaman. Haka kuma a binciki abin da ya sa ba a bi hanyar da aka saba bi ba wajen sayo makaman.

Ya ce ko da ma hayar jirgin aka bayar ai duk da haka jirgin mallakin mai shi ne. Saboda haka abin na da tayar da hankali in ji shi.To saidai wani Mataimakin Shugaban na CAN mai suna Rev. Shayibu Bely a ce sam Kirista ba su shirya wani makirci ga Musulmi, kuma ba su da wani makamin da ya wuce Littafi Mai Tsarki (Bible).

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG