Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Ci Gaba da Jimamin Mutuwar Ali Kwara


Marigayi Alhaji Ali Kwara
Marigayi Alhaji Ali Kwara

Tun rasuwar marigayi mai yaki da miyagun barayi, Alhaji Ali Kwara a ke ci gaba da nuna juyayin rashin sa, inda kafafen sadarwar yanar gizo su ka cika makil da ta'aziyar rasuwar mutumin da a ke aiyanawa a matsayin mai Jarumi.

Marigayin wanda ya rasu a Abuja, yayin da a ke shirin fita da shi kasar Masar don zuwa wani Asibitin na musamman, an yi jana'izar sa a garin sa Azare da ke jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya.

Alhaji Ali Kwara kan dade ba a ji duriyar sa ba, amma duk lokacin da ya fito ya kan nuna 'yan fashi da barayi da ma masu yin sojan gona da sunan sa wanda ya kan kama da damka su hannun 'yan sanda.

BAUCHI: Ali Kwara ya kama barayi masu fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane suna karban kudin fansa
BAUCHI: Ali Kwara ya kama barayi masu fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane suna karban kudin fansa

A wata zantawa, Ali Kwara ya damke wani mai sojan gona da sunan sa wanda ke cigaba da jagorantar 'yan banga a yanzu haka. Kwara ya baiyana dabi'un da za a iya tantance shi da 'yan bogi.

Wasu daga muggan 'yan fashi da wakilin sashen Hausa ya samu a gidan marigayin mai suna Na- Kutama, ya ce bai san adadin mutanen ya kashe ba.

Acan Azare kuwa, a na ci gaba da zuwa ta'aziyya. Malamin Islamiyya Sabbar Aminu makwabtan gidan Ali Kwara ne da a ka yi jana'izar da shi. Ya ce marigayin ya bar wasiya kafin mutuwarsa.

Shi ma mai sharhi a gidajen rediyo a Bauchi Almustapha Haji Sufi ya ce an yi babban rashin mutum mai gaskiya da amana.

Shin kowaye zai cike gurbin Ali Kwara, a daidai lokacin da lamuran rashin tsaro ke kwan gaba kwan baya?.

Domin Karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG