Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Wahalar Man Fetir a Najeriya


Masu ababan hawa mamaye da gidan mai domin sayen fetir a Legas
Masu ababan hawa mamaye da gidan mai domin sayen fetir a Legas

Ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin man fetir a wasu sassan Najeriya duk da cewa an shiga sabuwar shekara kuma gwamnati ta ce tana daukan matakan dakile karancinsa.

Rahotanni daga wasu sassan Najeriya na cewa har yanzu matsalar karancin man fetir da ta faro daga karshen shekarar 2017 na ci gaba da addabar wasu jihohin kasar.

Wannan kuwa na faruwa ne duk da matakan da gwamnati ta ce tana dauka na shigo da man daga kasashen waje da kuma yin yaki da masu boye shi.

Wannan lamari ya haifar da nuna yatsa tsakanin hukumomin kamfanin matatar man na NNPC da kuma kungiyar dillan man fetir din kasar ta IPMAN.

Wakilin Muryar Amurka a Abuja, Hassan Maina Kaina, ya aiko da rahoton cewa har yanzu ana samun layuka a gidajen man da ke babban birnin na Najeriya.

A jihar Kaduna ma, rahotanni na cewa lamarin haka yake, yayin da ‘yan kasar ke ci gaba da kokawa da tsadar rayuwa da karancin man ya haifar.

Matsalar karancin man fetir a Najeriya kan faru a duk karshen shekara.

Akan kuma zargi dillalan man ne da boye shi, domin cin kazamar riba, yayin da ake bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, zargin da suka sha musantawa.

Kamar yadda tarihi ya nuna, akan samu saukin matsalar da zarar an shiga sabuwar shekara.

Amma a wannan karon lamarin ya dauki wani sabon salo inda matsalar ta-ki ci ta-ki cinyewa, duk ko da matakan da gwamnati ta ce tana dauka.

A jawabinsa na shiga sabuwar shekarar 2018, shugaba Muhamamdu Buhari ya sha alwashin zakulo masu a haifar da wannan matsala.

Ya kuma dora alhakin karancin man a kan masu son yi wa gwamnatinsa zagon kasa domin a ga bakinta.

Najeriya na daya daga cikin kasashen duniya na gaba-gaba da ke da arzikin man fetir.

Amma matsalolin da suka jibinci matatun man da suka kwashe shekaru da dama ba sa aiki yadda ya kamata, da matsalar masu ta da kayar baya a yankin Niger Delta mai arzikin man, hade da masu boye fetir a irin wannan lokuta kan sa kasar a cikin halin ni-'yasu.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG