Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harbe-harbe a Abuja Ya sa Mutane Sauya Hanya


Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria
Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria

Sanadiyar harbe-harba a Abuja ya sa mutane dake kokarin zuwa aiki da safe sauya hanya.

Sanadiyar harbe-harba a Abuja ya sa mutane dake kokarin zuwa aiki da safe sauya hanya.

Harbe-harben da hantsi ya sa mutane sun shiga wani rudani. Amma mai magana da yawun hukumar SSS wato 'yansandan leken asiri tace wasu ne suka yi yunkurin arcewa daga inda aka tsaresu

Bincike ya nuna cewa wadanda ke tsaren sun yi wuf ne sun kwace bindigar wanda yake raba masu abinci lamarin da ya kai ga musayar wuta. Kawo yanzu dai babu labarin rasa rayuka ko kuma arcewar wasu.

Wani wanda ya taba zaman wakafi a hukumar ta SSS Abdullahi Aliyu daga Katsina ya bayyana yadda gidan wakafin yake. Yace shi an rufe masa ido an saka masa ankwa a hannu.Da ita yake kwana yakekuma tashi. Abinci kuma sau biyu ake basu. Dakunan da ake saka mutane suna da matukar sanyi.

A hukumar SSS ake tsare da wadanda ake zargin suna da hannun wurin kashe Sheikh Awwal Albany kuma ana zaton wadanda sune suka yi yunkurin arcewa.

Ga karin bayani
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG