Accessibility links

'Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria


Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria

Sheikh Abbas Isa Lauya Zaria yace 'yan bindigar sun kashe Sheikh Albani tare da matarsa da dansa a lokacin da suke komawa gida daga karantar da Sahih Buhari

Wasu 'yan bindiga sun bude wuta a kan motar daya daga cikin mashahuran malaman Sunni na Najeriya, Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria, suka kashe shi tare da matarsa da wani dansa.

An ce akwai wasu a cikin motar da suka ji rauni wadanda suke kwance a asibiti a yanzu haka.

Da yake tabbatarwa da Muryar Amurka abkuwar wannan abu, wani shaihin malami na Ahlus Sunna, Sheikh Abbas Isa Lauya, yace da misalin karfe 10 na daren asabar din nan, 'yan bindigar sun tare motar malamin suka kuma bude masa wuta, a lokacin da yake kan hanyar komawa gidansa daga wajen karantarwa.

Sheikh Abbas Lauya yace kamar yadda ya saba yi, Sheikh Albani ya je ya karantar da dalibai littafin Sahih al-Buhari, kamar yadda yake yi na sauran littatafan, sai ya kama hanyar komawa gida tare da iyalinsa.

A nan ne wadannan 'yan bindigar da ya bayyana su a zaman makiya Musulunci da Musulmi suka tare malamin suka kashe shi tare da matarsa da kuma wani dansa.

Tuni har mutane masu jimami da alhinin wannan abu sun fara kwarara cikin dare a kan babura da motoci, wasu da kafa, zuwa gidan shaihin malamin a Zaria domin nuna tsananin bakin cikinsu.

A yau lahadi ake sa ran za a yi jana'izarsa.

Ga cikakken bayanin da Sheikh Abbas Isa Lauya yi ma wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu Elhikaya\.

XS
SM
MD
LG