Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Saman Isra'ila Na Kawo Tsaiko A Yunkurin Da Iran Ke Yi Na Samun Mazauni a Syria - Babban Hafsan Sojin Isra'ila


Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence.

Wani babban hafsan sojan Isra’ila yace hare-haren da jiragen saman kasarsa suke kai wa a Syria sun takura yunkurin da Iran ke yi na samun mazauni a kasar

Amma kuma ita ma Isra’ila an gurgunta ta, har dole yanzu ita ma tana neman agaji kafin ta iya cimma burinta na ganin bayan Iran daga Syria din.

Wannan bayanin da kwamandan na Isra’ila, Maj-Gen. Michael Edelstein ya bayar jiya a wajen wata tattaunawa da wata cibiyar Yahudawa ta shirya a nan Washington, ya bada karin hasken da ba a saba samu ba, akan dabarun Isra’ila a kan Syria.

Haka kuma, da yake amsa tambayar da sashen Iraniyanci na gidan rediyon VOA yayi masa, Gen. Edelstein yace matakin kai hare-hare da Isra’ila ke dauka a can Syria da Lebanon da sauran kasashe na samarda nasara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG