Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Jamus Ta Zama Yar Amshin Rasha - Inji Trump


An fara taron kolin kungiyar kawancen tsaron NATO da gardama yau Laraba, yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya fara da caccakar Jamus, yana zargin kasar mafi girma, mafi arziki kuma a kungiyar tsaron NATO da cewa ta zama ‘yar amshin Rasha

A lokacin wata ganawa a wurin karin kumallo da sakatare-Janar din Kungiyar NATO, Jens Stoltenberg, Trump soki Jamus akan yadda ta bar wani kamfanin makamashin Rasha mai suna Gazprom ya sanya bututun iskar gas da ake kira Nord Stream 2 da turanci ya bi ta yankin tekun kasar.

Trump ya kuma yi ikirarin cewa, Jamus na biyan Rasha biliyoyin dala duk shekara.

Shugaba Trump ya tambayi mahalarta taron na NATO cewa “ta yaya za a kasance tare, idan wata kasa na samun makamashinta daga kasar da ake neman tsari da ita?

Jamus, a cewar shugaban na Amurka, ta watsar da masana’antun ta na gawayin kwal, ta watsar da nukiliyarta, tana kuma samun mai da gas masu yawa daga Rasha. Ya ce ina gani wannan wani abu ne da ya kamata NATO ta duba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG