Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hira Da Dan Takarar Jam'iyar People's Trust, Joel Gbenga Hashim


Dan takarar Shugaban kasa na Jam'iyar People's Trust, Joel Gbenga Olawepo Hashim
Dan takarar Shugaban kasa na Jam'iyar People's Trust, Joel Gbenga Olawepo Hashim

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyar People’s Trust Joel Gbenga Olawepo Hashim’ yace idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai gabatar da wani tsarin da zai inganta rayuwar mata da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da rage talauci.

A cakin hirarshi da Sashen Hausa, dan takaran yace zai samar da tsarin bada bashi mafi kankancin ruwa domin mata su sami jari su iya dogaro ga kai, su kuma taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.

Mr. Gbenga Hashim yace abinda yake haifar da talauci shine rashin bada dama ga wadanda suka fi rauni a tsakanin al’umma. Bisa ga cewarsa, ba mata Jari zai taimaka wajen rage rashin aikin yi taskanin matasa. Dangane kuma da ba mata mukamai a gwamnati, dan takarar na jam’iyar People’s Trust yace, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai ba mata abinda ya fi kashi arba’in cakin dari na mukaman siyasa.

Dangane kuma da harkokin tsaro, dan takaran yace, zai gabatar da wani tsarin dogarawan tsaro daban da ‘yan sanda ko soji da zasu taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro. Ya bayyana raunin amfani da sojoji da ake yi wajen yakar Boko Haram da yace rashin hukumta wadanda aka kama yasa aka gaza shawo kan tada kayar baya da suke yi.

Mr. Gbenga, wanda shine mataimakin kakakin jam’iyar PDP na kasa na farko, wanda bayan ficewarshi daga jam’iyar ya shiga harkokin kasuwanci a faninin albarkatun mai, kafin sake komawa siyasa, ya bayyana cewa, yana da kwarin guiwa jam’iyarshi zata taka rawar gani a babban zabe na kasa, bisa ga cewarsa, wadansu kananan jam’iyu sun bayyana janyewa su mara mashi baya.

Saurari cikakkiyar hirarsu da Alheri Grace Abdu

Hira da dan takarar shugaban kasa na Jam'iyar People's Trust:6:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG