Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hong Kong Ta Gudanar Da Babban Zaben Ta Na Farko


A Jiya Lahadi ne Hong Kong ta gudanar da babban zabenta na farko tun babbar zanga zangar ‘yan rajin dimokaradiyya a shekara ta 2014, a daidai lokacin da kiraye-kirayen ayyana 'yancin kai da kuma kyamar China ke yaduwa tsakanin matasa masu kada kuri'a.

Masu kada kuri’a dai sun zabi ‘yan Majalisu har 70, a inda masu rajin dimokaradiyya ke fatan su sami akalla sulusi, wato kashi ‘daya cikin uku, na ‘yan Majalisun, domin samun damar dakatar da duk wani yunkurin masu goyon bayan China a kokarinsu na samar da doka.

A wata karamar zanga zanga an bukaci shugaba Leung Chun-ying, wanda China ke marawa baya da yayi murabus, a wajen rumfar da ya kada kuri’a, yayin da wasu kuma ke bayyana kudurunsu na sa ido kan harkokin gwamnatinsa.

Ana dai kyautata tsamanin yau litinin za a fitar da sakamakon zaben.

Hong Kong dai ta zamanto fagen dambarwar siyasa tun zaben ‘yan Majalisar da aka yin a baya bayan nan a shekara ta 2012, wanda yayi sanadiyar fara babbar zanga zangar masu rajin kare dimokaradiya a shekara ta 2014.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG