Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hoton Yaron da Ya Ji Rauni A Aleppo Ya Tada Hankalin Kasashen Duniya


Hoton Omran Dangneesh dan shekara biyar da aka raunata ssnadiyar harin jirgin sama da aka kai kan birnin Aleppo dake kasar Siriya

Cikin shekaru biyar din ake ta gwabza fada a Siriya rayuka da dam sun salwanta kana dubban yara suka jikata

Hoton wani yaro kankanin yaro da ke da alamun raunukka a jikinsa, har da jinni, da aka ce ya samu daga farmakin jiragen sama da aka kai a birnin Aleppo na kasar Syria, ya tada hankalin jama’an kasashen duniya daban-daban da suka ga surar tahsi a cikin kafofin watsa labarai da suka hada da na duniyar gizo.

Kungiyoyin ‘yan adawar kasar ta Sham ne suka sako wannan hoton dake nuna yaron zaune akan kujerar wata motar daukar majinyatta, inda aka ganshi duk jinni da kura sun rufe jikin nashi.

Wani likitan garin na Aleppo, Osama Abu al-Ezz, yace sunan yaron Omran Dagneesh, kuma dan shekaru 5 ne kacal da haihuwa.Jiya aka kai shi assibiti, aka bashi magani kana aka sallame shi. Rahottani sunce an ji wa yaron ciwo ne a lokacinda wasu jirage suka kai farmaki akan wata unguwa ta ‘yan adawa dake garin na Aleppo.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG