Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hugo Maradona Kanen Diego Maradona Ya Rasu


Hugo Maradona
Hugo Maradona

Hugo Maradona, kanin Diego Maradona kuma tsohon dan wasan kwallon kafa ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 52.

Kulob din Italiya Ascoli ya ce ya mutu yau Talata a gidansa da ke Monte di Procida, kusa da Naples, sakamakon bugun zuciya

Napoli ta sayi kanin Maradona a cikin 1987 bisa rokon Diego aka aka ba da rancenshi ga Ascoli. Ya kuma buga wasa a Rayo Vallecano, Rapid Vienna da sauran kungiyoyi da dama a duniya. Ya zauna a yankin Naples.

Mutuwar Hugo ta zo ne watanni 13 bayan Diego Maradona ya mutu sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 60. Ya rasumakonni biyu bayan da aka yi masa tiyata a kwakwalwa.

"Shugaban kulob din Aurelio De Laurentiis, mataimakin shugaban kasa Edoardo De Laurentiis, jami'ai, ma'aikatan horarwa, 'yan wasa da dukan dangin SSC Napoli suna jimamin rashin, tare da dangin Maradona bayan mutuwar Hugo," in ji Napoli.

-AP

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG