Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Hisbah Ta Yi Barazanar Maka Jaruma Umma Shehu A Kotu


Umma Shehu, hagu da Sadiya Haruna, dama (Instagram/Umma Shehu/Sadiya Haruna)

“Me ye naku na shiga ku yi kane-kane saboda Sadiya Haruna tana wani abu mara kyau…ku ‘yan Hisban idan na ce zan kira suna ba za a ji dadi ba."

Rahotanni daga Kanon Najeriya na cewa, Hukumar Hisbah ta yi barazanar maka jarumar Kannywood Umma Shehu a kotu idan ba ta bayyana a gabanta ta yi mata karin haske kan zargin da ta yi wa hukumar ba.

A farkon makon nan Shehu ta zargi ‘yan hukumar ta Hisbah da yin shisshigi saboda ta kama Sadiya Haruna bisa zargin tana tallata hajjarta a shafukan sada zumunta ta hanyar amfani da kalamai da hotunan batsa.

Sadiya Haruna ta taba shiga harkar shirya fina-finan Kannywood kafin daga baya ta janye.

Yanzu ta kan sayar da kayan mata ne da na shafe-shafe a shafukan sada zumunta.

“Me ye naku, na shiga ku yi kane-kane saboda Sadiya Haruna tana wani abu mara kyau…..ku ‘yan Hisban idan na ce zan kira suna ba za a ji dadi ba, akwai masu neman matan su ma.” Shehu ta fada a wani bidiyo wanda ga dukkan alamu ta riga ta goge shi daga shafinta idan har a nan ta wallafa.

Sai dai rahotanni daga Kano sun ce Kwamandan hukumar ta Hisba Harun Sani Ibn Sina, ya gayyaci jarumar ta ‘Gidan Badamasi’ da ta gurfana a gabanta don ta yi masu karin haske kan zargin da ta yi.

Kokarin jin ta bakin jarumar ya ci tura a lokacin hada wannan rahoto, sai dai abu na baya-bayan nan da ta wallafa a shafinta na Instagram hade da wani hoto na cewa, “‘Yar Shehu sai gani,” sannan ta saka hotunan ido.

Jama’a da dama kan zargi hukumar ta Hisbah wajen rashin kamanta adalci yayin gudanar da ayyukanta, inda ake cewa ta fi huce fushinta akan talakawa yayin da take kau da idonta daga abubuwa da masu hannu da shuni ke yi.

Sai dai a lokuta da dama, hukumar ta Hisbah ta sha musanta wannan zargi da ake mata.

Tuni dai hukumar ta Hisba ta sako Sadiya Haruna.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG