Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar JAMB Ta Gabatar Da Yin Rijistar Kai A Lagos Da Abuja


Hukumar Shirya Jarabawa ta JAMB
Hukumar Shirya Jarabawa ta JAMB

Za a bullo da wuraren yin rijista don yin jarrabawar da akafi sani da suna Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) da kuma Direct Entry (DE) na 2022 a Abuja da Legas.

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ce ta sanar da hakan a cikin sanarwar ta na mako-mako da ta fitar a ranar Litinin da ta gabata, a cewar shugaban sashen yada labaran ta, Dr Fabian Benjamin.

Ya bayyana cewa ci gaban yana cikin yunƙurinsa na yin amfani da ƙwarewar yanar gizo na ƙara yawan masu neman ilimin kwamfuta. Hukumar ta JAMB dai ta yi fatan cewa, wannan sabon tsarin da aka bullo da shi zai rage cunkoson jama’a a jarrabawar da ake yi na kamputa wato Computer Based Test (CBT) a garuruwan biyu.

"An tsara wannan kyakkyawan shirin ne, don fadada wuraren samun rajistar da zai yi daidai da bin ka'idojin COVID-19," in ji shi.

Hukumar ta kuma sanar da daukar lambar '66019' a matsayin karin kuma lambar USSD na zabi baya ga lambar '55019' wacce ke aiki tun 2018, don rajistar UTME/DE da sauran muhimman ayyuka.

Ya yi bayanin cewa dalilin yunƙurin shine don sauƙaƙe aikin rajista na 2022 UTME/DE ta hanyar tabbatar da cewa ba shi da wahala ko kaɗan ga dalibai, musamman a yanayin da yawancinsu ke aika sakon buƙatun lambar na USSD guda.

A cewar JAMB, dalibai masu neman shiga jarabawar 2022/23 UTME/DE za su yi amfani da lambobin biyu don ƙirƙirar bayanansu don rajista.

"Kamar yadda aka saba, ana buƙatar daliban su aika da Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN) zuwa kowace ɗaya daga cikin waɗannan lambobin USSD don cire bayanansu daga bayanan NIMC kafin su ci gaba zuwa kowace cibiyar da aka amince da su don kama kwayoyin halittar yatsosinsu," in ji shi.

XS
SM
MD
LG