Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kidayan Jama'a ZataTantance Masu Ilimin Zamani


Hukumar kidayan jama'a tace zata dauki tsawon watanni ukku domin gudanar da aikin a duk fadin Najeriya. A shekarar 2013 tayi irin wannan aikin amma akan fannin kiwon lafiya.

Barister Aliyu Datti shine kwamishinan hukumar mai kula da jihar Niger yayi Karin haske akan wannan aikin.

‘’Muna son mu san matsayin ilmi a duk wannan kasa tamu yau ana yin wannan abu, zamu sa yaran mu su zagaya a duk fadin jihar su bincika domin jin me yasa wadanda yakamata ace suna makaranta basu makaranta domin muyi kokari muba hukuma wannan bayani abinda ke jan ilmin baya, kowa aka samu ana iya cewa kai nan gidan ku mun lura akwai yan shekaru 15 zuwa 40 suna zaune me yasa haka, a ciki zaka ga mutum ya fara makaranta primary bai gama sai mu tambaya me yasa bai gama ba, duk yadda ya fada zamu rubuta wasu zaka ga sun gama sakandare basu iya ci gaba ba, ya fadi jarabawa ne ko kuma rashi ne.

To sai dai da aka tambaye shi ko zasu rika cewa a kawo takardun ne su gani ko kuwa iya bayani za ayi musu su rubuta?

Anan sai Aliyu Datti yace ‘’Bayani zaiyi muna musali sai muce kana da takardan sakandare, sai muce mr yasa baka je University ba sai yace banci jarabawa ba ko kuma banda hanyar da zan tafi, shikenan sai mu rubuta, ba zamu ci gaba da wata tambaya ba, amma ba aikin mu banemu tantance cewa ko kana da takardan ko baka dashi, mu dai muji me yasa baka samu ci gaba ba.”

Shima shugaban karamar hukumar Rafi Mohammed Sahabudden Isah yayi Karin haske akan muhimmacin wannan aiki a hukumance da kuma tasirin sa a fannin ilmin.

‘’A wannan kudiri da ita hukumar kidaya ta dauka na batun tantance shaanin batun ilmi yana da muhimmamci kwarai da gaske sabo da halin da ilmi ya shiga a wannan kasa tamu ta Najeriya musammam ma kananan hukumomi ada karkaran mu, watau wata hanyace da aka kirkiro domin a samu dama ayi tambayoyi ga su yara da iyaye abinda ya shafi shaanin ilmi musammam ma ilmi mataki na farko a karamar hukuma wasu makarantu suke zuwa me yasa suka fita makaranta, yaya ainihin makarantun suke ciki’’

Masana dai na ganin ba a makara ba a wajen gudanar da wannan aikin duk ko da cewa fannin ilmin ya dade da shiga wani hali musammam a yankin arewacin Najeriya.

Hukumar Kidayar Jama'a - 2'58"

XS
SM
MD
LG