Hukumar kula da yan gudun hijiran ta Najeriya ta samar da kayakin karatu ne da kuma injunan nika ga yan gudun hijiran da bala'in rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu,da yanzu haka ke sansanonin da aka tanadar na Malkohi, da Damare da kuma Fufore a jihar Adamawa.
Da take jawabi wajen raba kayakin, shugabar hukumar ta NCFRMI,Hajiya Sadiya Umar Faruq,wadda daraktan kula da yan gudun hijira Lawal Hamidu ya wakilta,tace manufar tallafin shine sake tada komadar ‘yan gudun hijiran ta hanyar basu abun koyon sana’a tare da kula da ilimin ‘ya’yansu.
Shima a jawabinsa jami’in kula da sashin karantarwa na rundunan soji ta 23 dake Yola,wanda yake kula da karantar da yan gudun hijiran,Kaftin Danjumi ya yaba da tallafin da hukumar yan gudun hijiran ta samar tare da yin kira ga sauran kungiyoyi da hukumomi da suma su tallafa.
‘’ Wannan tallafi ne dake da muhimmanci ga wadannan ‘yan gudun hijira,kuma mu a namu bangare zamu ci gaba da bada gudummawa wajen karantar da wadannan yara,don suma su sami ilimi a matsayinsu na manyan gobe,’’ a cewar jami’in sojin.
Tun farko a jawabinsa,babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa, ADSEMA, Alhaji Haruna Hamman Furo,ya ce kullum a shirye suke su bada nasu hadin kai wajen ganin an tallafawa wadannan yan gudun hijiran,kana ya bayyana kokarin da gwamnatin jihar keyi a yanzu.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz
Facebook Forum