Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe A Nijer Ta Fara Ganawa Da Masu Fafutuka Kafin Zabe FEB. 21


Jami'an hukumar zabe ta CENI

Hukumar zaben jamhuriyar Nijer na ci gaba da tuntubar rukunonin al’umar kasar da nufin tattara shawarwarin da zasu bada damar gudanar da zaben shugaban kasa na ranar 21 ga watan Faburairu cikin kyaukyawan yanayi.

Akan haka ne shugabanin hukumar ta CENI suka yi wani zama da shugabanin kungiyoyin fararen hula da na kafafen yada labarai da hantsin yau Laraba.

Sanin tasirin gudunmuwar da kungiyoyin fararen hula da kafafen yadada labarai ke bayarwa wajen tsare tsaren zabe da gudanar da shi har i zuwa lokacin fitar da sakamako ya sa shugabanin hukumar CENI shirya wani taron da ya hada bangarorin uku a kan teburi domin neman shawarwarin su a wannan lokaci na shirye shiryen zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Nijer na ranar 21 ga watan da muke ciki.

Kakakin hukumar zabe Malan Nafiou Wada, ya ce muhimmiyar rawar da kungiyoyin fararen hula da kafafen yada labarai ke takawa wurin sa ido a kan zabe da kuma wayar da jama’a a kan yanda zasu kada kuru’un su ne yasa hukumar CENI ta gayyato su domin nuna musu irin matsalolin da hukumar ta gano da kuma gudnmuwar da zasu bayar wurin shawo kan matsalolin.

Maida hankali wajen ayyukan horar da jami’an zabe na daga cikin matakan da ‘yan rajin kare dimokaradiya suka shawarci hukumar zabe a kan su, koda yake wani bangare na wannan aiki abu ne da ya rataya a wuyan jam’iyun siyasa inji shugaban kungiyar CADDED Son Allah Dambaji.

Ya ce “matsalolin da aka samu a baya sune rashin bada horo a kan yanda aiki yake a runfar zabe wanda galibi ‘yan saiysa ne ke bada su, kana a lokacin da yakamata su bada horon basu yi bayar ba har sai da lokaci ya kure. Haka zalika itama CENI tana da nata matsala na ba jami’anta horon ranar daya wanda bashi wadatarwa.”

Karancin kayayyakin zabe da ma rashin kayayyakin a wasu yankunan na daga cikin matsalolin da aka yi fama da su a zabubukan watan Disamban da ya gabata dalili kenan shugabar kungiyar kare hakkin mata ta CONGAFEN Hadjia Fatima Kako ta zo da wannan shawara.

Shugabanin hukumar zabe sun ce su da kansu sun lura da akasarin matsalolin da mahalarta wannan taro suka nuna damuwa akansu kuma a cewar su sun dauki matakai inda tuni aka fara isar da kayayyakin zabe zuwa jihohi yayin da ake shirin soma zaman horon jami’an zabe a ranekun 13 da 14 ga watan da muke ciki.

Ga dai rahoton wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
XS
SM
MD
LG