Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Fara Bincike Kan Harin Cocin Jihar Ondo


Akalla mutane 50 Ake Kyautata Zato Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Wani Mummunan Harin Coci A Jihar Ondo, Najeriya
Akalla mutane 50 Ake Kyautata Zato Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Wani Mummunan Harin Coci A Jihar Ondo, Najeriya

Ranar Litinin 6 ga watan Yuni hukumomi a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya suka kaddamar da bincike kan mummunan harin da aka kai a wata cocin Katolika.

WASHINGTON, DC - Takamaimai hukumomi basu bayyana adadin mutanen da aka kashe a harin na cocin St Francis Catholic Church ba a jiya Lahadi, amma kakakin gwamnatin jihar Ondo ya fada wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa ‘yan bindigar sun kashe mutane 21, shi kuma kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci wani likita a jihar Oyo da ya ce mutanen da suka mutu sun kai 50.

An kai wadanda suka jikkata a harin asibitocin yankin don jinya, yayin da ‘yan sa-kai suka kaddamar da aikin neman masu bada gudummuwar jini don taimaka wa wadanda suka jikkata.

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya lashi takobin daukar mataki a kan lamarin ya kuma bada umarnin a sassauto da tutoci kasa a jihar don karrama wadanda harin ya shafa.

Maharan dai sun kai farmaki ne a lokacin da ake wani taron sujada na musamman a ranar Lahadi wanda ake kira "Pentecost Sunday" da turanci inda suka yi amfani da bindigogi da bamabamai.

Fadar Vatican ta ce Paparoma Francis ya yi wa wadanda harin ya shafa addu’a da kuma Najeriya.

Nan take dai ba a tabbatar da ko su waye suka kai harin ba. Yayin da akasarin yankunan Najeriya ke fama da matsalolin tsaro, jihar Ondo na daga cikin jihohin kasar da ke zaune lafiya. Ko da yake jihar ta sha fuskantar tashin hankalin manoma da makiyaya.

XS
SM
MD
LG