Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin kasar Pakistan sun tsare matar Bin Laden da kuma 'yarshi


Hukumomin kasar Pakistan sun tsawata tsaro a gidan Osama bin Laden

Kafar watsa labaran kasar Pakistan tace hukumomin kasar suna tsare da matar shugaban al-Qaida Osama bin Laden da kuma yarshi wadanda suke cikin gidan da sojojin kundumbalar Amurka na musamman suka kashe shi ranar litinin da asuba.

Kafar watsa labaran kasar Pakistan tace hukumomin kasar suna tsare da matar shugaban al-Qaida Osama bin Laden da kuma yarshi wadanda suke cikin gidan da sojojin kundumbalar Amurka na musamman suka kashe shi ranar litinin da asuba. Rahoton ya ambaci ta bakin jami’an leken asirin kasar Pakistan na cewa, matar bin Laden ‘yar kasar Yemen da ‘yarshi mai shekaru 12 suna daga cikin mata da dama da kuma kananan yara da ake tsare da su bayan sumamen da Amurka ta kai birnin Abbottabad. Tashar talabijin ta ABC news ta Amurka sun bayyana sunan matar a matsayin Amal Ahmed Abudul Fatah, yayinda kafar sadarwar kasar Pakistan ta buga hoton passpo dinta jiya Laraba. Sakataren watsa labarai na fadar White House Jay Carney ya bayyana ranar Talata cewa, matar bin Laden tayi kokarin shiga gaban sojojin kundunbalar Amurka aka kuma harbeta a kafa amma ba a kashe ta ba. Rahoton ya kuma ambaci ta bakin jami’an kasar Pakistan cewa, yarinyar ‘yar shekaru 12 ta shaidawa hukumomi cewa tana gani aka harbi mahaifinta aka kashe shi kafin aka tafi da gawarshi.

XS
SM
MD
LG