Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Qaida Ta Tabbatar Da Kisan Osame Bin Laden


Shugaba Barack Obama na Amurka yake magana da wasu ma'aikatan wani kamfani a jihar Indiana.

Kungiyar ta al-Qaida tayi bayanin tabbatar da kisan ne a shafinta na Intanet mai sunan Jihadist yau Juma’a.

Wani lokaci a yau juma’a ce shugaba Barack Obama na Amurka zai ziyarci sansanin sojin Amurka dake Fort Campbell jihar Kentucky domin tattaunawa da iyalan jaruman sojin kundubalar Amurka da suka kai harin kisan Osama Bin laden shugaban kungiyar al-Qaida.

Babban makasudin kai ziyarar shine gaisuwa da godiyar nuna jaruntakar da sojin suka yi. An shirya shugaba Barack Obama zai gana da sojin a kebe kafin ya fito bainar jama’a yayi jawabi.

A halin da ake ciki, kungiyar al-Qaida ta bada sanarwar tabbatar da kisan shugabanta Osama bin Laden.

Kungiyar ta al-Qaida tayi bayanin tabbatar da kisan ne a shafinta na Intanet mai sunan Jihadist yau Juma’a.

XS
SM
MD
LG