Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Barazanar Fallasa Barayin Biro a Sudan Ta Kudu


South Sudan
South Sudan

Hukumar tara kudaden shiga ta kasar Sudan ta Kudu tana barazanar fallasa jami'an gwamnati da na bankuna da suka saci kudaden shiga.

Hukumar tace ta tara sama da dala miliyan tara a watan Fabrairun wannan shekara ta dubu biyu da goma sha tara, idan za a kwatanta da dala miliyan hudu da dubu dari bakwai da aka tara a watan janairu, sai dai kwamishinan hukumar Olympio Attipoe yace har yanzu akwai jami'ai kalilan masu halin bera da suke karkatar da kudi mai yawa zuwa bankunan ajiyar kashin kansu.

Ya ce nan ba da dadewa ba, hukumar tara kudaden shigar zata fallasa sunayen jami'an.

Watan da ya gabata, hukumar tara kudaden shigar tace ta tara sama da fam biliyan daya da kuma dala miliyan hudu bayanda ta kirkiro wani tsari na tara kudaden shigar da ake samu daga wadansu kafofi daban da albarkatun man fetur.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG