Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Maroko Sun Kama Mutane 30 Da Ake Zargi Da Safarar Jarirai


Hukumomin kasar Maroko sun kama mutanen 30 a wannan makon a birnin Fes bisa zargin safarar jarirai.

WASHINGTON, D. C. - Kamfanin labarai na kasar ta Arewacin Afirka, MAP, ya ruwaito a ranar Laraba cewa wadanda ake zargin, wadanda suka hada da jami'an tsaro, likitoci, ma'aikatan jinya da sauran kwararrun kiwon lafiya an kama su ne a farkon wannan makon.

Ana tuhumar su da hadin baki da iyaye mata wadanda ba su da aure don sayar da jarirai ga iyalan da ke son daukar yara.

Rahoton ya ce shirin nasu ya kuma hada da cin zarafi, zamba da kuma satar magungunan da ba a sayar da su ba tare da takardar likita ta sayan magani ba. Ana zargin wasu da taimakawa wajen saukaka zubar da ciki, abinda ya sabawa ka'idojin kasar Morocco, idan ba da gaggawa ba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG