Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Pakistan Sun kama Mutane Hudu Dangane Da Kisan Wata Mace Mai Juna Biyu a Lahore


Mustafa Kharal, lauyan Farzana Paveen, wacce danginta suka kashe saboda ta auri wanda ranta yake so.

Cikin wadanda suke hanu harda mahaifinta da kawunta da wasu 'yan uwanta su biyu.

‘Yansanda a Pakistan sun ce sun kama mutane hudu dangane da kisan wata mace mai juna biyu, wacce wasu danginta suka lakada mata duka suka kashe ta, domin ta auri mutuminda take so.

‘Yansanda suka ce an daki Farzana Parveen ‘yar shekaru 25 da haifuwa, da duwatsu da tubali a harabar wata kotun kasar dake birnin Lahore ranar talata da ta shige, yayinda take dakon bada shaida gaban alkali, cewa da son ranta ta auri mijinta.

Jiya jumma’a ‘Yansanda suka ce sun kama kawunta da wasu ‘yan uwanta biyu ranar Alhamis. Tuni dama suka damke mahaifinta bayanda ya amsa laifin yana da hanu a kisan nata.

‘Yansanda sun dauki wannan matakin ne kwana daya bayanda PM kasar Nawaz Shariff ya fidda sanarwar inda ya bukaci babban minister mai kula da lardin Punjab da birnin Lahore yake karkashisa ya dauki matakai kan wannan batu. Haka shima babban jojin kasar Tassaduq Hussein Zailani shima ya bukaci babban baturen ‘Yansandan kasar ya gabatar masa da rahoto kan wannan kisa.

Mijin Farzana ya gayawa manema labarai cewa ya roki ‘Yansanda da suke kusa cewa don Allah su hana dukar matarsa, amma basu yi komi ba yayinda danginta suke dukanta. Amma baturen ‘Yansandan a Lahore ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ‘Yansanda basa wurin lokacinda dangin Farzana suka kai mata hari.

Shima mijin nata Iqbal Mohammed, yana da tarihi wajen gallazawa mata. Ya amince ya kashe matarsa ta fari, amma ba a daure shi ba, saboda danginta sun gafarta masa.
XS
SM
MD
LG