Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Tsaro A Amurka Sun Cafke Matar Wanda Ya Kashe Mutane 49 A Orlando


Omar Mateen mutumin da ya kashe mutane 49 ya kuma raunata wasu 50
Omar Mateen mutumin da ya kashe mutane 49 ya kuma raunata wasu 50

Anan Amurka hukumomi suka ce an kama matar Omar Mateen wanda ya kai hari kan wani klub a birnin Orlando dake jahar Florida. Ana zarginta da rashin gaskiya da kawowa shari’a cikas.

Atoni Janar ta Amurka Loretta Lynch jiya Litinin ta tabbatar da kama Noor Salman. An kama ta kusa da birnin San Francisco inda take da zama da danta. Masu gabatar da kara suka ce yau Talata suke sa ran gabatar da ita a karon faro a gaban kotu, a yankin Oakland dake jahar California.

Salman ta juma 'Yansanda suna gudanar da bincike a kanta, tun bayan da mijinta ya bude wuta a wani klub mai farin jini ga 'yan luwadi cikin watan Yunin bara ya kashe mutane 49, ya raunata 50 a wani hari da ake ganin ya sami ingizawar kungiyar ISIS.

Mijin nata Omar Mateen 'Yansanda sun harbeshi har lahira bayan sa'o'i uku ana kai komo tsakaninsa da jami'an tsaro.

'Yansanda a birnin na Orlando da hukumar FBI suna ta kokarin sanin ko Salman tana da masaniya gameda harin.

XS
SM
MD
LG