Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Nan Da Rai Na - In Ji Baba Ari


Dan wasan barkwanci na Hausa, Aminu Ali Baba Kofar Nassarawa, wanda aka fi sani da suna Baba Ari.

Aminu Ali Baba Kofar Nassarawa, mai wasan fina-finan ban dariya na Hausa, yace yana nan da rai, kuma cikin koshin lafiya.

Shahararren dan wasan barkwanci na Hausa, Aminu Ali Baba Kofar Nassarawa, wanda duniya ta sani da sunan "Baba Ari" ya ce yana nan da ransa, kuma cikin koshin lafiya, a bayan da wasu suka yi ta yada jita-jitar mutuwarsa a kan dandalin mu'amalar nan ta Facebook dake yanar gizo.

A tattaunawar da yayi da filin "A Bari Ya Huce..." da za a yada ranar asabar 22 ga watan Yuni, Baba Ari yace shi kansa ya ji mamaki da ya fara samun kiraye-kirayen jama'a kamar makonni biyun da suka shige, inda ake ta ba shi wannan labari cewar ai an zata ya mutu.

Dan wasan yace a yanzu ya daina hulda baki daya a kan Facebook, ya kuma ce ba ya da dangantaka da wasu daga cikin masu sanya suna irin nasa a dandalin na Facebook in ban da wasu kannensa guda biyu maza.

A kasance da shirin na "A Bari Ya Huce..." a ranar asabar 22 ga watan Yuni a shirinmu na karfe 6 na safiya agogon Najeriya, domin jin cikakken bayanin wannan hira.

Ga somin-tabi.
Baba Ari Yana Magana Kan "Mutuwar" Da Aka Ce Yayi - 00:28
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:28 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG