Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Samun Sauki - Trump


Shugaban Amurka Donald Trump a sabon bidiyon da ya sake a ranar Asabar 3 ga watan Oktobar 2020. (Foto: Gedung Putih via Reuters)
Shugaban Amurka Donald Trump a sabon bidiyon da ya sake a ranar Asabar 3 ga watan Oktobar 2020. (Foto: Gedung Putih via Reuters)

Wani sabon bidiyo da Shugaban Amurka Donald Trump ya sake daga asibitin Walter Reed inda ya je jinyar cutar COVID-19, ya nuna halin da shugaban ke ciki bayan da aka kai shi asibitin a ranar Juma'a.

Shugaban Amurka Donald Trump ya saki wani sabon bidiyo daga asibiti inda ya ce ya fara samun sauki kuma nan ba da jimawa ba zai koma harkokinsa na yau da kullum.

Cikin bidiyon mai tsawon minti hudu, shugaban na Amurka ya kara da cewa, a lokacin da aka ba shi gado a asibitin sojoji na Walter Reed a ranar Juma’a, “bai jin dadi,” bayan da ya kamu da cutar coronavirus.

Amma ya kara da cewa, “a yanzu ina jin dama-dama” kuma “muna aiki tukuru domin na komo bakin aiki,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito.

A cewar Trump, yana da zabin ya zauna a Fadar gwamnati ta White House ya kare kansa, amma babu yadda za a yi a matsayinsa na shugaban kasa “ya kulle kansa a daki a sama.”

Shugaban na Amurka ya kuma mika godiyarsa ga likitoci da masu jinya da ke ba shi kulawa da kuma shugabannin kasashen duniya da Amurkawan da suka mika sakoninsu na fatan alheri.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, likitan Trump, Dr Sean Conley ya ce shugaban na "ci gaba da murmurewa" kuma yana samun lafiya tun bayan da aka gano yana dauke da cutar ta COVID-19.

Da sanyin safiyar ranar Juma'a Trump ya bayyana cewa shi da mai dakinsa Melania sun kamu da cutar ta COVID-19.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG