Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Ce Kemfen Zai Kare Ne Sa'o'i 24 Kafin Zabe


Manyan Jami'an INEC
Manyan Jami'an INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta INEC tace jami’iyyun siyasa zasu ci gaba da yakin neman zabe kamar yanda doka ta tanadar. Hukumar zaben ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta shirya a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya fadawa ‘yan jarida da masu sa ido a kan zabe daga sassa dabam-daban na duniya da suka halarci taron manema labaran cewa hukumar sa kimtsa sosai domin gudanar da zaben, ta kuma tabbatar da matakai domin kaucewa abin da ya faru a baya.

Farfesa Mahmood Yakubu ya yiwa wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka karin bayani yana mai cewa, abubuwa da suka faru a bay aba zasu sake faruwa ba saboda sun koyi darasi a kana bin da ya faru a baya. Yace akwai zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da shugabannin kananan hukumomi, zasu yi amfani da darasi da suka koyi su tabbatar da gani ba a sake ganin abin da ya faru a makon jiya.

Shugaban na hukumar ya amsa tambayoyin mahalarta taron ya kuma yi karin hake a kan batun lokacin yakin neman zaben ‘yan siyasa, inda yake cewa dokar kasa ta bawa ‘yan siyasa dama su yi yakin neman zabe har izuwa sa’o’I ashirin da hudu kafin a yi zabe.

An yita rade-radin an kama kayan zabe a wasu da ba ‘yan hukumar zaben ba ne, biyo bayan dage zaben a makon da ya gabata, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce bai da labarin wannan batu, don haka idan wani nada shaida zai iya kawo masa, amma abubuwa da aka watsa a yanar gizo suna da yawa.

Shugaban hukumar zabe Farfesa Yakubu ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa zasu yi aiki tsakanin su da Allah kuma ma’aikatar hukumar zasu isa runfuna zabe a kan lokaci, haka zalika ya yi alkawari ba za samu rashin kayan aiki a karkara ba.

Ga rahoton A’isha Mu’azu daga birnin Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG