Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Na Mutunta Yarjajjeniyar Nukiliya - In Ji Hukumar Saka Ido


Yukiya Amano, Shugaban Hukumar IAEA

Babu wasu hujjoji da ke nuna cewa Iran ta cigaba da yinkurin kera makaman nukiliya bayan shekarar 2009.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido akan makaman nukiliya ta ja hankalin duniya yau Talata akan wani rahoto da daraktanta ya gabatar a shekarar 2015, wanda ya nuna cewa babu wasu kwararan alamu da ke nuna cewa Iran na wasu take-take da ke da alaka da kera makaman nukiliya bayan shekarar 2009.

Rahoton, wanda shugaban hukumar ta makamashin ‘Atom’ ta kasa-da-kasa da ake kira IAEA a takaice, Yukiya Amano ya gabatar, ya kawo karshen binciken da aka kwashe fiye da shekaru 10 ana yi game da zarge-zargen cewa Iran ta yi yinkurin kera makaman nukiliya, abinda Iran din ta sha musantawa.

Rufe binciken na zaman wani bangaren yarjejeniyar da Iran ta cimma da Amurka, da Burtaniyya, da China, da Faransa, da Rasha, da Jamus na takaita shirin nukiliyarta saboda ta sami sassaucin takunkumi.

Mr. Amana ya lura cewa Iran ta yi wasu ayyuka da ke da alaka da kera wasu abubuwa masu fashewa da karfin nukiliya, kafin shekarar 2003. Amma wadannan ayyukan ba su wuce nazarin kimiyya ba da kuma samun kwarewar fasaha.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG